Sunday, 28 April 2019

Yanda wata mata ta dauki nauyin karatun wani almajiri daga firamare har zuwa jami'a

Wannan wani almajirine, Dan Yakubu da wata baiwar Allah, Hajiya Fatima A. Modibbo ta dauki nauyin karatunshi daga firamare har zuwa jami'a. Yayi karatu a jami'ar Maiduguri inda ya karanci fannin tattalin arziki.Yanzu haka dai ya kammala karatun nashi har ya fara bautar kasa a jihar Bayelsa. 

Tun yana dan shekaru 6 aka kaishi almajirci jihar Kano inda a nanne ya hadu da Hajiya Fatima, ta hadu dashi inda ta daukeshi ta sakashi a makaranta, kamar yanda ta bayar da labari.

No comments:

Post a Comment