Monday, 22 April 2019

Yanda za'a duba sakamakon jarabawar Jamb ta wayar hannu

Hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a ta Jamb ta bayyana cewa dalibai da suka rubuta jarabawar su kwantar da hankulansu kada su sake wani Cafe ko gurin da aka musu rijistar jarabawar su musu wayau wajan duba sakamakon jarabawar, da kansu zasu iya duba sakamakon a wayoyin hannunsu.Me kula da harkar labaran hukumar, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyanawa Punch haka inda yace basu saki sakamakon jarabawar ba zuwa yanzu, har yanzu suna kokarin ganin sun tantance jarabawarne da kuma gano wadanda suka yi satar jarabawar, yace idan sun saki sakamakon jarabawar zasu sanar.

Yace nan da sati me zuwa suke sa ran sakin sakamakon jarabawar.

Ya kara da cewa sun saukake duba jarabawar ta yanda za'a iya dubawa ta wayar hannu. Yace dalibai miliyan 1.8 ne suka rubuta jarabawar kuma duk wanda suka kama da satar jarabawa bawai maki 100 za'a cire mai ba kamar yanda ake yayatawa, a'a jarabawar tashi ce gaba daya za'a soke

No comments:

Post a Comment