Wednesday, 17 April 2019

'Yar shekara 15 ta sakawa mijinta dan shekara 33 gubar bera a abinci


Wata mata me suna Hassana Lawal 'yar kimanin shekaru 15 ta sakawa mijinta, Sale Abubakar dan kimanin shekaru 33 gubar bera a binci.

Lamarin ya farune a kauyen Bechi dake karamar hukumar Kumbotso jihar Kano.

Bayan zubawa mijin nata gubar beran an garzaya dashi asibitin Murtala dake Kanon sannan ita kuma 'yansanda sun kamata, kamar yanda kakakin 'yansanda na jihar, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar a sanarwar da ya fitar jiya,Talata.

Yace da misalin karfe 2 na ranar Talata suka samu rahoton sannan auna kan bincike wanda idan aka kammala zasu mika wadda ake zargo a kotu.

No comments:

Post a Comment