Sunday, 14 April 2019

'Ya'yana 4 jikoki 27>>Inji Daso

Tauraruwar fina-finan Hausa wadda ke fitowa a matsayin uwa, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso, ta baiwa masoyanta dama a shafinta na dandalin Instagram inda tace su mata duk tambayar da suke so zata basu amsa.A cikin tambayoyin da aka mata, wani ya tambayeta me yasa ake kiranta da Daso?

Sai tace mai saboda Alherine.

Wata kuma tambayeta 'ya'yan ta nawa sannan jikokinta nawa?

Sai tace 'ya'yana 4, jikoki 27.

Wasu sun mata tambayar shin wai da gaske ita jakadiyar sarkin Kano ce?

Saidai Daso bata amsa wadannan tambayoyi ba inda tace abune wanda ya shafeta ita kadai.

Sannan wani ya tambayeta me yasa take fim alhalin tana da aure?

Sai ta bashi amsar cewa ai a kowace sana'a da aiki akwai ma'aurata.

Gadai wani yanki daga cikin yanda tambaya da amsar ta kasance:


No comments:

Post a Comment