Saturday, 18 May 2019

'Abin da ya sa nake auri saki': 'Allah ya bani komai dana rokeshi amma banda mace'>>Adam A. Zango

Shahararren dan wasan Hausa nan, Adam A Zango ya shaida wa BBC dalilin da ya sa yake yawan auran mata kuma daga bisani ya sake su.


Dan wasan ya ce ba kasa zama yake yi da mace ba, "ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba."

Ya kuma ce: "Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa."

Daga nan, Zango ya danganta batun da kaddara daga Ubangiji inda ya ce: "Allah Ya ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace."


No comments:

Post a Comment