Thursday, 9 May 2019

ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI


NA DAYA,  SADUWA DA MACE DA GANGAN AZUMI YA KARYE KUMA SAI ANYI KAFFARA . BUKHARI DA MUSLUM 
NA BIYU, CIN ABINCI DA GANGANCI,  AZUMI YA KARYE SAI ANYI RAMUWA DA KAFFARA .
NA UKU,  SHAN RUWA DA GANGAN, AZUMI YA KARYE SAI ANYI RAMUWA DA KAFFARA .
NA HUDU,   KAKARO AMAI FA GANGAN 
Abu Dauda da Tirmiziy 
NA BIYAR,   ZUWAN JININ ALADA KO JININ HAIHUWA, ANA CIKIN AZUMI. DA IJMAIN MALAMAI. 

NA SHIDA,  GANGANTA FITAR MANIYI TA HANYAR KALLO KO RUNGUMA,  KO KISS KO KALLON FINAFINAN BATSA. Mazahabar Malik da Ahmad bin Hambal 
NA BAKWAI,   FASA NIYAR AZUMI BAYAN MUTUM YA DAUKO AZUMI YAYI NIYAR FASAWA AZUMI YA KARYE RUNDA BABU NIYYA. IJMAIN MALAMAI. 
NA TAKWAS,  YIN RIDDA DA FITA MUSULUNCI ANA AZUMI,  AZUMI YA KARYE3TUNDA BABU ADDINI. 
NA TARA,  YIN ALLURAR DA TAKE ZAMA KAMAR ANCI ABINCI. IBN USAIMEEN .
YIN KARYA DA GULMA DA SHARRI DA KAZAFI DA ASHARIYA, SA ZAMAN CACA, DA LUDO,  DA KARTA,  DA KALLON FINNFINAN BATSA,  DA MUSU,  DUKA WADANNAN SUNA TAUYE AZUMI, YA ZAMA MUTUM YA SHA KISHIRWA AMMA BABU LADA. 

ALLAH YA TSARE MANA AZUMIN MU , YA KUMA SA YA ZAMA KARBABBE.
Malam Aminu Ibrahim Daurawa.

No comments:

Post a Comment