Monday, 6 May 2019

Akalla mutum 41 ne suka mutu a wutar da ta kama jirgin sama

Fasinjoji akalla 41 ne suka mutu bayan wani jirgin saman Rasha ya yi saukar gaggawa kuma ya kama da wuta a filin jirgin saman Sheremetyevo da ke birnin Moscow.


Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna fasinjoji na saukar gaggawa don kubuta daga cikin jirgin saman Aeroflot lokacin da ya tsaya yana cin wuta.

Kafofin yada labarai a Rasha sun ce akwai kananan yara biyu da wani ma'aikacin jirgi a cikin wadanda suka riga mun gidan gaskiya.


Wani shaida ya ce sai wanda "Allah ya yi wa gyadar dogo" a ce wani ya kubuta daga jirgin, wanda ke dauke da fasinja 73 da ma'aikatan jirgi biyar.

Shugabar ma'aikatar lafiyar Rasha, Veronika Skvortsova ta fada a cikin wata sanarwa cewa an kai mutum shida asibiti - uku cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Kamfanin jiragen saman Aeroflot malakar Rasha ya ce jirgin ala tilas ya dawo filin jirgi "saboda wasu dalilai", amma bai fayyace ba.

Jirgin saman, kirar Sukhoi Superjet-100, ya tashi daga filin jirgin saman Sheremetyevo da karfe 18:02 agogon kasar inda ya nufi birnin Murmansk.

Ma'aikatan jirgin sun aika da sakon shiga halin gigita lokacin da "nakasu" ya faru jim kadan bayan tashinsa.

Bayan ya yi saukar gaggawa ne a filin jirgin, sai injinan wannan jirgi suka kama wuta a kan hanyar sauka da tashi, a cewar kamfanin Aeroflot.

Ma'aikatan jirgin "sun yi duk abin da za su iya yi don kubutar da fasinjojin," wadanda aka fitar da su a cikin dakika 55, in ji kamfanin.

Daga cikin mutum 78 da ke cikin jirgin Superjet-100, 37 ne kadai aka gani, a cewar kwamitin bincike na Rasha.

Kamfanin Aeroflot ya wallafa jerin sunayen mutanen da aka san sun kubuta ya zuwa yanzu, ya kara da cewa za a ci gaba da sabunta jerin sunayen da zarar an samu wani karin bayani.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment