Saturday, 11 May 2019

Akwai 'yan Najeriya miliyan 30 da basu taba ganin wayar hannu ba

Shugaban kungiyar masu kamfanonin sadarwa na Najeriya, Olusola Teniola ya tabatar da cewa akawai dumbin mutane a kauyukan kasarnan da basu taba ganin wayar hannu ba.Yayi wannan bayanine a yayin da yake hira da jaridar Punch inda aka tambayeshi ko akwai wasu yankunan Najeriya da har yanzu basu da fasahar wayar hannu?

Yace tabbas akwai domin bincikensu ya nuna cewa akwai 'yan Najeriya miliyan 30 dake zaune a kauyuka da basu taba ganin wayar hannu ba ballan tanama su yi amfani da ita.


No comments:

Post a Comment