Thursday, 16 May 2019

Akwai yiwuwar dakatar da Man City daga Champions League


Manchester City
Manchester City ta ce "ba ta ji dadi ba amma ba ta yi mamaki ba" bayan an kai karar ta gaban kwamitin hukumar kwallon kafa ta Uefa mai kula da kuma kayyade harkokin kudi.


A farkon wannan makon ne sashen wasannin BBC na turanci ya ruwaito cewa masu bincike na hukumar Uefa na son a dakatar da City daga gasar Zakarun Turai ta kaka guda idan aka same ta da laifin ketare iyakar tsarin kashe kudi na FFP.
Jagoran masu bincike Yves Leterme ya bayyana abin da yake son a yi, amma babu tabbas ko yana goyon bayan dakatarwa.
Man City ta ce "zarge-zargen ketare iyaka ba gaskiya ba ne".
Rahoton ya zargi City ta ketare iyakar hukumar Financial Fair Play bayan da ta yi aringizo a wata yarjejeniyar daukar nauyi.
An ci ta tarar ta fam miliyan 49 saboda irin wannnan laifi da ta aikata a 2014.
Uefa ta ce: "Bayan tattaunawa da mambobin kwamitin binciken Leterme yanke shawarar kai Man City kara zuwa kwamitin kula da kuma kayyade harkokin kudi na CFCB bayan ya kammala bincikensa".
"Ba za mu sake yin wata magana ba kan batun har sai an sanar da hukuncin da kwamitin CFCB ya yanke."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment