Friday, 10 May 2019

An bai wa Aminu Ado Bayero sarautar Bichi

Wasu majiyoyi masu karfi daga gidan sarautar Kano da kuma gwamnatin jihar, sun tabbatar wa BBC cewa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Aminu Ado Bayero sarautar daya daga cikin sababbin masarautun da aka kirkiro a Kano.


An bai wa dan marigayi Sarki Ado Beyeron sarautar Bichi ne a ranar Juma'a.

Wani na kusa da sabon sarkin Bichin da ya bukaci a boye sunansa ya tabbatar wa BBC lamarin ya kuma ce tuni Aminu Bayeron ya karbi sarautar.

Mai martaba sabon sarkin Bichin shi ne Wamban Kano a yanzu, kuma yana daya daga cikin manyan 'ya'yan marigayi Ado Bayero.

Nan gaba ne dai ake sa ran za a sanar da nadin nasa.

Sauran sarakunan sababbin masarutun za su kasance wadanda ke kan karagarsu ne a yanzu.

Wasu bayanai dai sun nuna cewa tuni 'yan gidan sarautar Kano suka yi ta kamun kafa a wajen gwamna don ganin an nada su sarautar.

A ranar Laraba ne Gwamna Ganduje ya sanya hannu kan dokar da majalisar dokokin jihar ta gabatar a ranar Litinin, ta neman kara yawan marautun jihar.

Lamarin dai ya janyo ce-ce ku-ce a tsakanin al'ummar kasar baki daya ba ma na Kano ba kawai.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment