Monday, 13 May 2019

An baiwa tauraron dan kwallon Chelsea dakatarwar watanni 20


Wata kotu a kasar Ingila ta dakatar da dan wasan Chelsea, Danny Drinkwater har na tsawon watanni 20 daga tukin mota bayan amsa laifinshi da yayi na yin tuki alhalin yana cikin maye.


Kotun ta kuma bukaci dan wasan da yayi aikin sakai wanda ba lada na tsawon awanni 70 da kuma biyan tarar fan 170.

A ranar 8 ga watan Afrilu ne 'yansanda suka kama Drinkwater bayan da ya afkawa wani gini ya kuma rusa katangar ginin da motarshi kirar Range Rover akan hanyarshi ta dawowa daga mashaya.

No comments:

Post a Comment