Thursday, 16 May 2019

An daurawa yaran da basu kai shekaru 18 ba aure a kasar Amurka da yawansu yakai 200,000


Wani rahoto ya bayyana cewa an samu auren yara kanana da basu kai shekaru 18 da haihuwa ba da yawansu yakai 200, 000 a kasar Amurka a cikin shekaru 15 da suka gabata.

Rahoton na Independent UK yace yaran sun yi amfani da wasu damarmaki dake cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Amurka wajan yin auren nasu. Daga ciki akwai yara mata 'yan shekaru 10 da kuma wani yaro shima dan shekaru 11 da suka yi auren.

A dokar kasar ta Amurka za'a iya daurawa kananan yara da basu kai shekaru 18 ba aure idan aka samu cikar wasu sharudda kamar daukar ciki da kuma amincewar iyaye.

No comments:

Post a Comment