Sunday, 12 May 2019

An kaddamar da Kur'anin da aka rubuta da zinari da siliki a Afghanistan

Wani masanin zane ɗan ƙasar Afghanistan ya buɗe Kur'ani mai girma da ya shirya a cikin shekaru biyu da zinari da siliki a cikin watan Ramadan.An buɗe Kur'anin ne a gidan tarihin Firoz Koh dake Kabul babban birnin Afghanistan.

Masanin zane Muhammed Tamim Sahibzadeh, ya bayyana cewar duk da aiki ne tuƙuru ya samu nishaɗantuwa a lokacin rubuta Kur'anin.

An dai yi amfani da sanadarai da dama domin rubuta wannan Kur'anin mai nauyin kilo 8.6 da shafuka 610. Yana da kuma siffofi irin ba Kur'anan ƙarni na 15 da 16.

Sahibzadeh,  ya bayyana cewar ya yi amfani da siliki mai tsawon mita 305 domin rubuta ayoyin Alkur'anin da suka kunshi zinariya da tagulla.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment