Friday, 17 May 2019

An kama mutane 80 a Kano da laifin cin abinci da rana a watan Ramadan

Hukumar Hizba dake Kano ta bayyana cewa ta kama mutane 80 bisa laifin cin abinci da rana a watannan na Azumin Ramadana.Hukumar tace ta kama mutanen ne a bangarori daban daban na jihar inda aka samesu suna cin abinci da rana kiri-kiri.

Me magana da yawun hukumar, ya bayyanawa BBC cewa duka wadanda suka kama musulmaine dan Azumi baya hawa kan wanda ba musulmi ba.

Ya kara da cewa wadanda aka kama din sun rika karyar cewa wai basu ga wata bane wasu kuma suce basu da lafiya amma daga baya duk an gane cewa karya suke.

Yace sun gargadi wadanda aka kama din da cewa idan aka sake kamasu za'a gurfanar dasu a gaban kotu sannan suka sakesu, lura da cewa wannan shine karin farko da suka aikata laifin.

No comments:

Post a Comment