Wednesday, 8 May 2019

An Karya Sandar Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Bisa Hayaniya Da Ta Kaure A Zauren Majalisar

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dage zaman ta sau biyu a yini daya ba tare da aiwatar da komai ba saboda rigingimu masu nasaba da shugabanci.


Shugaban Majalisar, Alhaji Isah Idris Gwaram, ya fara karanto abubuwan dake kunshe cikin jadawalin al’amuran da Majalisar za ta gudanar a yau amma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Suleiman Ibrahim Gwiwa, ya cira hannun tare da fadin cewa yana da hanzari kafin a yi wani abu.

A daidai wannan lokacin ne wasu daga cikin"yan majalissu  suka karya sanda Majalisar gida uku domin nuna kin amincewar su da ci gaba da zaman Majalisar.

Rigingimun dai ba za su rasa nasaba da kudirin neman gyaran fuska ga wasu tanade-tanaden zaman Majalisar da ya hadar da cewa duk shugaban Majalisar da mataimaki da shugaban masu rinjaye da na marasa rinjaye da gagarabadan Majalisar da aka taba tsigewa to ba za a sake zabensu akan wadannan matsayin ba.

Haka kuma gyaran fuskar dake kunshe cikin jadawalin Majalisar na yau ya hadar da gyaran doka ta 3 da tanadi na 5 (3) akan tsarin yadda za a zabi sabbin shugabannin Majalisar, yayin da wadanda suka goge a harkokin Majalisar kadai za su iya neman shugabanci banda sabun shiga.

Kasancewar an karya sandan Majalisar, sai shugaban Majalisar  Alhaji Isah Idris Gwaram ya dage zaman Majalisar zuwa karfe uku na rana domin tabbatar zaman lafiya da bin doka da oda.

Bayan sake dawowa zaman Majalisar da karfe uku ne, sai shugaban Majalisar Alhaji Isah Idris Gwaram ya sanar da dakatar da gabatar da rahoton Kwamatin agajin gaggawa da kuma yin karatu na daya akan kudirin neman gyaran fuska ga dokar da ta kafa kwalejin ilimin addinin musulunci da nazarin harkokin sharia da ke Ringim wadda su ma ke kunshe cikin jadawalin abubuwan da Majalisar za ta gudanar.

Daga nan sai shugaban Majalisar ya sanar da dage zaman Majalisar zuwa ranar Alhamis 9 ga watan nan.
Rariya.


No comments:

Post a Comment