Thursday, 2 May 2019

An rabawa makafi manhajar karatun Alkur'ani a Najeriya

An rarrabawa makafi a Najeriya Alkur'ani na musamman wanda zai saukaka masu karatu da hada.


Wata kungiyar agaji ta kasar Qatar ce ta rarraba Alkur'ani wanda aka yi shi don makafi da masu matsalar makanta.

Daruruwan makafi mata da maza ne daga jihohin daban-daban na kasar suka samu karbar Alkur'anin, a lokacin bikin rarraba shi da aka yi a birnin Abuja.

Kur'anin na makafi dai zai ba su damar koyon karatu da sauraron karatun Alkur'ani da kuma tafsiri a cikin harsunan ingilishi da faransanci da kuma larabci.


Daliban da suka samu kyautar Kur'anin sun fito ne daga jihohin Nasarawa da Niger da Filato da Katsina da kuma birnin tarayyar Najeriya wato Abuja.

Hamdu Muhammad Abdu shi ne shugaban kungiyar agaji ta kasar Qatar ya ce an raba wannan kur'ani na zamani ga makafi domin ba su damar zabin sura ko tafsiri a harsunan Ingilishi da Faransanci da Larabci.

Ya ce nan gaba za su kuma ziyarci Sokoto da Borno da kuma Kano

Daliban da suka samu gajiyar wannan Kur'anin sun bayyana cewa zai taimaka masu wajen hadda da tilawa ba kamar a baya ba da dole sai an samu mai karantar da su.

Jabir Almajir malami ne a daya daga cikin makarantun jihohin da suka samu wannan gajiya, ya ce wannan tallafi da aka basu ya tabbatar da cewa duniyar musulunci ba ta manta da su ba.

Ya ce kur'anin zai kawo masu sauki wajen karantar da dalibai.

Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari da manyan malaman da suka halarci bikin sun bukaci wadanda suka samu gajiyar kyautar da su luzumnci karatun Al-kura'ni musamman a watan Ramadan da ke tafe.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment