Thursday, 2 May 2019

An yi garkuwa da dalibai mata a arewacin Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun far wa wata makarantar sakandire ta 'yan mata a jihar Zamfara ake arewacin Najeriya tare da yin garkuwa da dalibai da dama.


Jaridun kasar sun bayar da labarin cewar 'yan bindiga sun kutsa kai makarantar sakandire ta 'yan mata dake Moriki tare da bude wuta a sama inda suka kuma yi garkuwa da wasu daga cikin daliban.

Wata majiya ta bayyana cewar maharan da ba su iya kai wa ga dakunan kwanan daliban ba sun yi garkuwa da masu dafa abinci 4 da malamai 2.

An bayyana cewar 'yan bindiga sun rufe hanyar dake zuwa garin kafin daga baya da daddare su kai hari makarantar.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 'yan ta'addar Boko Haram sun yi garkuwa da dalibai mata a makaranytar Sakandire dake Chibok a jihar Borno.

Duk da cewar gwamnatin Najeriya ta yi yunkurin ganin an saki daliban amma har yanzu ana fadin cewar akwai wasu 112 a hannunsu.

A ranar 19 ga Fabrairun 2018 ma 'yan ta'addar na Boko Haram sun yi garkuwa da wasu mata dalibai su 109 a garin Dapchi dake jihar Yobe. Bayan wasu 'yan kwanaki 'yan ta'addar suka saki daliban amma suka ci gaba da rike Leah Sharibu da ta ki ta furta ta bar Addinin Kiristanci.

DN


No comments:

Post a Comment