Wednesday, 15 May 2019

Antoine Griezmann ya bar Atletico Madrid: Akwai yiyuwar ya koma Barcelona


Tauraron dan kwallon Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya bayyana aniyarshi ta barin kungiyar. A wani bidiyo da shafin sada zumunta na kungiyar ya wallafa, Griezmann yayi bankwana da kungiyar inda yace shekaru 5 kenan, ina godiya bisa dukkan abubuwan da kukai min bazan taba mantawa da kuba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Griezmann na shirin komawa Barcelona ne nan bada dadewa ba. Saidai a kakar wasan data gabata ne dan wasan ya ki yadda da komawa Barca inda ya ce Athletico ce gidanshi.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko da gaske zaije Barcelonar?  

No comments:

Post a Comment