Thursday, 9 May 2019

Atiku ya bayyana hanyar da Najeriya zata yi maganin matsalolinta

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019 da ya gabata,Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hanyar da za abi wajan magance matsalar Najeriya.Atikun ya bayyana hakane a shafinshi na Twitter inda ya kawo ayar Qur'ani da Allah madaukakin sarki ke cewa, Ya ku wanda kuka yi imani, An wajabta muku Azumi kamar yanda aka wajabtawa wanda suka gabace ku tsammanin zaku yi takawa.

Atiku ya kara da cewa, Najeriya zata yi maganin kalubalenta ta hanyar Addu'a, Azumi da gaskiya.


No comments:

Post a Comment