Sunday, 19 May 2019

Ba mu amince a bai wa jihohi biliyan 649 ba>>NLC

Kungiyoyin kwadago da na fararen hula a Najeriya, sun shawarci gwamnatin kasar da ta jinkirta mikawa gwamnatocin jihohi cikon rarar kudinsu na Paris Club da yawansu ya kai Naira biliyan dari 649 har zuwa lokacin da za a rantsar da sabbin gwamnatoci a ranar 29 ga watan Mayun da muke ciki.Kiraye-kirayen kungiyoyin dai na zuwa ne bayan sanarwar minister kudin kasar Zainab Ahmed da ke bayyana cewa, gwamnatin na gab da mikawa jihohin cikon kudaden wanda shi ne kaso na karshe da ake mayar musu tsawon lokaci.

A bangaren kungiyar kwadago ta NLC ta ce kamata ya yi gwamnati ta jira zuwa kafuwar sabbin gwamnatoci a matakan jihohi don ganin kudaden sun amfani al'umma.

Ko a bara dai akwai zarge-zarge da ya dabaibaye yadda gwamnaonin suka kashe wani kaso na kudin, wanda tun farko shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bukaci su yi amfani da shi wajen biyan hakkokin ma’aikata.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment