Monday, 6 May 2019

Babban dan wasan Barcelona ba zai buga karawarta da Liverpool ba

Me horas da 'yan wasan Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana kaduwa da ciwon da tauraron kungiyar, Ousmane Dembele ya samu a wasan da suka buga da Celta Vigo ranar Sabar din data gabata wanda suka tashi Celta Vigo na cin 2-0.Dembele ya ji rauni yayin da yake gudu a wasan na ranar Asabar amma ba'a canjashi ba sai bayan mituna 4. Ernesto Valverde yace be saka Coutinho ba dan gudun kada ya sake jawowa kanshi wata matsala.

Binciken raunin Dembele da aka yi jiya, Lahadi ya tabbatar da cewa bazai buga wasan Liverpool da Barcelona ba na zagaye na biyu na kusa dana karshe na cin gasar Champions League.

Ernesto Valverde dai yaki saka manyan 'yan wasanshi a wasan na Asabar wanda ya ajesu dan shirin sake haduwa da Liverpool.

No comments:

Post a Comment