Tuesday, 14 May 2019

Bamu da hannu a maganar yiwa Gwamnatin Buhari juyin mulki>>Sojoji

Hedikwatar tsaro ta kasa ta fito ta nesanta kanta daga yunkurin yiwa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari juyin mulki da wata kungiya me suna NCP ke kwarmatawa.Hedikwatar tsaron ta hannun mataimaki daraktan labarai, Capt. Muhammed Wabi ta fito nesanta kanta daga wata sanarwa da kungiyar ta watsa dake cewa za'a yiwa Buhari juyin mulki sannan a saka gwamnatin rikon kwarya.

Yace mutane su yi watsi da wannan labari sannan su yi Allah wadai dashi kuma sojoji suna biyayya ga Najeriya da kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito.

No comments:

Post a Comment