Wednesday, 15 May 2019

Bance Ronaldo da Messi basu cancanci lashe kyautar Ballon d' Or ba>>Aguero

Tauraron dan wasan Manchester City Sergio Aguero ya karyata rade-radin dake yawo cewa wai yace Ronaldo da Messi basu cancanci lashe kyautar gwarzon dan kwallo ta Ballon d' Or ba.Wani labari ya watsu dake cewa Aguero yace wanda zai lashe kyautar ta Ballon d' Or kamata yayi ya fito daga kungiyoyin Liverpool ko Tottenham da suka kai wasan karshe na gasar Champions League.

Saidai a martaninshi, Aguero yace shi be fadi waccan magana ba. Abinda yake so shine indai Messi na taka leda kuma lura da yanda ya taka leda a kakar wasa ta bana to shine ya cancanci lashe kyautar ta Ballon d' Or.

Aguero dai abokine na kusa ga Messi.

No comments:

Post a Comment