Sunday, 12 May 2019

'Bani da gida ko asusun ajiya ko kasuwanci a kasar waje'


Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ba shi da asusun ajiya ko gida ko kuma wani kasuwanci a kasashen waje.
Jonathan na mayar da martani ne ga sabon zargin da lauyoyin gwamnatin Najeriya suke mashi a wata kara da suka shigar a wata kotu da ke Landan kan cinikin rijiyar mai na bogi da aka fi sani da cinikin Malabu.


Goodluck
Gwamnatin Najeriyar dai na zarginsa da da karbar rashawa a cinikin bogin da ya gudana a baya.
A wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai bashi shawara kan harkokin watsa labarai Ikechukwu Eze, Jonathan ya ce zargin da ake yi mashi karya ce wacce dama an taba jinta tun a baya.
A karar da gwamnatin ta shigar, ta bayyana cewa wannan cinikayyar ba a yi ta kan ka'ida ba kuma an tsara ta ne bisa son rai.
Gwamnatin dai ta bukaci manyan kamfanonin mai na Eni da Shell da su biya ta diyyar dala biliyan 3.5 sakamakon bata mata suna.
Batun cinikin malabu ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya a can baya ganin cewa rijiyar man da aka yi cinikinta na daya daga cikin manyan rijiyoyin mai mafi daraja a Afirka.
Tun a baya dai, kamfanin Shell da kamfanin Italiya ENI sun kulla wata yarjejeniya da gwamnatin Najeriya don mallakar rijiyar mai, mai lamba OPL 245, wato wata makekiyar rijiyar mai da ke gabar ruwan yankin Neja-Delta da ke Najeriya.
Daga nan ne sai gwamnatin Najeriya ta mika kudin ga wani kamfani mai suna Malabu, wanda Mista Etete yake tafiyarwa kamar yadda masu gabatar da kara a Italiya suka bayyana a baya.
Wasu bayanai da masu gabatar da kara a Italiyar suka gabatar sun yi zargin cewa an halatta kudin haram da suka kai dala miliyan 466 ta hanyar biyo da su ta kasuwar 'yancin kuxi, inda daga nan aka mika wa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da wasu mukarrabansa.
Sai dai har yanzu, Jonathan din na musanta irin wadannan zarge-zargen.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment