Saturday, 25 May 2019

Barcelona ta ce za ta iya sayar da Reis kan kudi har Yuro miliyan 100

Kungiyar Kwallon Kafa ta Spaniya Barcelona ta sanya kudi har Yuro miliyan 100 ga dukkan kungiyar da take son sayen dan wasanta Ludovit Reis da ta saya daga hannun kungiyar Groningen tare da sanya hannu na shekaru 3 da shi.


Sanarwar da aka fitar daga Kungiyar Barcelona ta ce, ta sanya hannu da Ludovit har nan da watan Y8unin 2022 kuma yana da zabin kara wa'adin idan yana so.

Sanarwar ta kara da cewar, ta saka Yuro miliyan 100 don sakin Reis da ta karba daga hannun kungiyar Groningen ta kasar Holan kan kudi Yuro miliyan 3 da dubu 250.
Trthausa.No comments:

Post a Comment