Tuesday, 14 May 2019

Baturen Birtaniya ya karbi rashawa a wata badakalar Najeriya

Kotu a Faransa ta samu wani lauya dan asalin kasar Birtaniya da laifin karbar rashawa a badakalar Halliburton wadda ta shafi kulla kwangilar hako iskar gaz a tsibirin Bonny Island a Najeriya.Kotun wadda ta yi zamanta a unguwar Vesailles da ke birnin Paris ta ce, ta samu Jeffrey Tesler lauya da ke zaune a birnin London da laifin bayar da rashawa domin samun kwangila, inda ta ci shi tarar Euro dubu 30, kuma kafin nan wata kotun Amurka ta same shi da irin wannan laifi har ta yanke masa hukuncin daurin watanni 21 a gidan yari.

To sai dai lauyansa Thierry Marembert, ya ce zai daukaka kara a gaban kotun tarayyar Turai, yana mai cewa sam ba a yi wa wanda yake karewa adalci ba.

Ita dai kotun ta ce, ta samu lauyan dan kasar Birtaniya da karbar kudaden da yawansu ya kai Dala milyan 130 a matsayin tukuici daga kamfanonin da suka samu wannan kwangila ta hako iskar gaz a tsibirin na Bonny Island, kwangilar da a jimilce aka kiyasta cewa ta Dala milyan dubu 6 ce a Najeriya.

Kamfanoni hudu ne aka bai wa wannan kwangila, da suka hada da KBR wanda reshe ne ga Halliburton, kamfanonin da ake zargi da rashawa a gaban kotunan da dama na kasashen Turai.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment