Thursday, 16 May 2019

Bayan kammala gasar Premier League Pogba ya je aikin Umrah


A yayin da aka kammala gasar Premier League 'yan wasa nata tafiya hutu, tauraron dan kwallon Manchester United, Paul Pogba ya je kasar Saudiyya dan yin aikin Umrah.

An ga hoton Pogba da dan wasan Chelsea Kurt Zouma a kasa me tsarki kamar yanda Pogban ya saka a shafinshi na sada zumunta. Pogba ya rubuta a jikin hotunan da ya saka cewa kada ka taba mancewa da abubuwa masu muhimmanci a rayuwarka.

A karshen kakar wasannin Premier League biyu da suka gabata duk saida Pogba ya ziyarci kasa me tsarki.

No comments:

Post a Comment