Saturday, 18 May 2019

Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga na 7 a jere: Ribery da Robben sun fashe da kuka yayin bankwana da kungiyar

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta lashe kofin Bundesliga na 7 a jere bayan data lallasa Eintracht Frankfurt da ci 5-1. Gaba daya Munich ta lashe kofin sau 28 kenan.

Kafin take wasan an gabatar da taurarin kungiyar biyu, Franck Ribery da Arjen Robben dan zasu yi bankwana da kungiyar bayan kammala wannan kakar wasan a gaban 'yan Kallo. Duka su biyun sun rungumi juna suka fashe da kuka yayin bankwana da kungiyar.No comments:

Post a Comment