Saturday, 4 May 2019

Binta kofar Soro ta rasu: Karanta sakonta na karshe da ya dauki hankula

Tauraruwar fina-finan Hausa da ke fitowa a matsayin uwa, Binta Kofar Soro ta rasu, Manyan jaruman fim din Hausa irin su Ali Nuhu da Rahama Sadau da sauransu sun nuna Alhinin rashin nata.Wani sako da marigayiyar ta saka a shafinta na Instagram kwanaki biyu da suka gabata ya dauki hankula inda akaita yadashi.

A sakon Bintar ta roki yafiyar mutane wanda ta wa laifi da wanda bata wa laifi ba inda a karshe ta yi fatan Allah ya yafemana.

No comments:

Post a Comment