Sunday, 5 May 2019

Buhari ya dawo Najeriya


Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan bayan wata ziyara ta kashin kansa da ya kai a watan da ya gabata.


Jirgin shugaban ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 6:24 na yammaci.
Bayan isowar shugaban, sakataren watsa labaransa Femi Adesina ya fitar da wata sanarwa inda yake shagube ga 'yan adawa da cewa ''Bayan rubuce-rubuce da 'yan adawa ke yi na cewa shugaban bai da lafiya kusan likitoci biyar sun bashi shawara ya tsaya a duba lafiyarsa, a yanzu sai su hadiye kalamansu domin shugaban ya dawo.''
Tun bayan tafiyar shugaban, mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya bayyana cewa kwanaki goma zai yi kuma ba hutu zai je yi ba inda ya bayyana cewa zai rinka gudanar da ayyuka da can.
Shugaban ya tafi Landan din ne bayan ya kaddamar da wasu ayyukan ci gaba a fannonin ilimi da lafiya da hanyoyi a jihar Borno.
Sai dai tun bayan tafiyar shugaban, abubuwa da dama sun faru a Najeriyar da suka ja hankalin jama'ar kasar.
Abubuwan sun hada da:
BBChausa.

No comments:

Post a Comment