Thursday, 16 May 2019

Caccakar masu bayar da abincin Azumi suna daukar hoto su yada: Bada Hadiza Gabon nike ba>>Nazir Sarkin Waka

Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Wakar Sarkin Kano ya fito inda ya wanke kanshi da cewa ba da Hadiza Gabon yake ba a kalaman da yayi a farkon fara Azumi inda ya kalubalanci masu bayar da abincin Azumi suna dauka suna sakawa a shafukan sada zumunta.

Yace masu mai fassarar cewa da Hadiza Gabon yake basu fahimceshi ba kuma su ji tsoron Allah su daina yada karya dan ana cikin watan Azumine.

No comments:

Post a Comment