Wednesday, 1 May 2019

Champions League: Barca ta ci Liverpool 3-0: Messi ya ci kwallo ta 600: Barca ta ci kwallo ta 500 a gasar: Magoya bayan Liverpool na caccakar Suarez da Mane

Barcelona ta lallasa Liverpool daci 3-0 a wasan da suka buga na kusa dana karshe a gasar cin kofin Champions League a daren yau, Luis Suarez ne ya fara ciwa Barcelona wasa sannan sai Messi ya ci sauran kwallaye biyun daga baya.
Wannan ce kwallon Suarez ta farko a kakar wasa ta bana a gasar ta Champions League bayan da yayi ta kai hari har sau 36. Sannan kwallon da ya ciwa Barca itace ta kawo yawan kwallayen da Barcelonar ke da su zuwa 500 a gasar Champions League, wannan yasa Barcar ta kamo babbar abokiyar takararta, Real Madrid wadda tuni ta wuce wannan mataki inda yanzu ita take da yawan kwallaye 551 a gasar.

Murnar cin kwallon da Suarez yayi ta baiwa wasu magoya bayan Liverpool haushi inda suka ce be kamata yayi murna dan yaci Liverpool din kwallo ba saboda tsohuwar kungiyarshi ce, saidai tun kamin wannan wasa Suarez ya fadi cewa idan yaci Liverpool zai yi murna.

Shima Lionel Messi ya kamo babban abokin takararshi, Ronaldo a yawan kwallaye, inda kwallayennan biyu da yaci na yau suka kai yawan kwallaye 600 kenan da ya ciwa Barcelona a tarihi, ya fara ciwa Barca kwallone shekaru 14 da suka gabata.

Magoya bayan Liverpool sun rika caccakar Sadio mane saboda tureshi da Gerard Pique yayi a lokacin da yaje gidan Barca yake kokarin buga kwallo kuma sanadiyyar turewar ya fadi kasa, saidai a yayin da ake tunanin Gerard Pique ya jiwa Mane rauni, sai kawai akaga Mane din yayi zumbur ya tashi an ci gaba da kwallo, wannan yasa wasu magoya liverpool din suka rika cewa ai da ya sani ya kwanta saboda a basu bugun fenaret.

Hakanan magoya bayan Liverpool sun rika korafi akan wani tsutsu da yayi ta gittawa a cikin filin wasan yayin da ake tsaka da wasa.

Yanzu dai a wasa na gaba Barca zata ziyarci Liverpool.

No comments:

Post a Comment