Wednesday, 15 May 2019

Cushen Kwaya: Gwamna Ganduje yawa wadanda aka sako daga kasar Saudiyya kyautar miliyan 6 jimulla

Gwamnan jihar Kano,Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa inda suka gana da 'yan Najeriyarnan da akawa cushen kwayoyi a kayansu kuma kasar Saudiyya ta kamasu amma daga baya aka sakesu, gwamnan ya musu sha tara ta arziki.Gwamna Ganduje yawa Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar da aka sako daga kasar Saudiyya kyautar Miliyan 3 kowannensu, miliyan 6 jimulla kenan.

Muna tayasu murna.
No comments:

Post a Comment