Wednesday, 1 May 2019

Cutar farankama ta kama mutane sama da 700 a Amurka

Tun daga farkon shekara zuwa yau mutane 704 ne suka kamu da cutar farankama a yankunan Amurka daban-daban da suka hada da New York.


Sanarwar da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka ta fitar ta bayyana cewar, a ranar Litinin din nan an samu kamuwa da cutar a jihohin Amurka da dama.

Sanarwar ta ce, a New York da jihohi 22 na Amurka daga farkon 2019 zuwa yau cutar ta kama mutane 704.

Sanarwar ta kuma ce, mutane 44 ne sun kamu da cutar a lokacinda suka tafi zuwa wasu kasashen waje kuma mafi yawan wadanda suka kamu da ita mabiya darikar Orthodox ta Addinin Kirista ne da ba sa son allurar riga-kafi.

Sanarwar ta kuma ce, ya zuwa yanzu babu wanda cutar ta yi ajali amma dai an kai wasu 66 zuwa asibiti wadanda ake kula da su.

A wannan shekarar cutar ta yi kamari a Amurka yadda ba a taba gani ba a cikin shekaru 25.
TRthausa.


No comments:

Post a Comment