Wednesday, 1 May 2019

Dalilin da yasa muka jinkirta gayawa Duniya labarin 'Yaruwata>>Hajara 'yar uwar Zainab da aka sako daga kasar Saudiyya

'Yar uwar matashiyar da jami'an kasar Saudiyya suka kama bisa zargin ta'ammuli da miyagun kwayoyi wadda daga baya aka gano bata da laifi kuma gwamnatin tarayya ta saka baki aka sakota, Zainab Aliyu, watau Hajara kenan. Ta yi hira da BBC inda ta bayyana dalilin da yasa basu bayyana lamarin na 'yar uwarta ba tun tuni.Wasu Rahotanni sun bayyana cewa tun a watan Disamba na shekarar data gabata jami'an kasar Saudiyya suka kama Zainab Aliyu amma labarin be fito fili ba sai cikin 'yan kwanakinnan.

BBC ta tambayi Hajara shin ko me yasa suka boye wannan labari? Sai Hajara tace sun yi gudun yanda jami'an kasar Saudiyya zasu dauki lamarinne shiyasa basu yi gaggawar bayyanawa Duniya ba  sai yanzu.

Da aka tambayeta ya ta ji lokacin da aka kama 'yar uwarta, ta bayyana cewa, abin bai misaltuwa ta shiga tashin hankali, ta kara da cewa a lokacin da 'yar uwartata take kulle bata iya kiranta lokacin da take so saidai idan ita Zainab dince ta nemeta.

Ta bayyana cewa ta shiga cikin farin ciki mara misaltuwa bayan da aka saki 'yaruwartata.

No comments:

Post a Comment