Monday, 13 May 2019

Diyar Mohamed Salah ta dauki hankula bayan da ta ci kwallo a filin wasan Liverpool


Bayan tashi daga wasan Liverpool da Wolves jiya, Lahadi inda Liverpool din taci 2-0. Kamar yanda yake a al'ada, a duk wasan karshe, 'yan wasa sukan zo da iyalansu, haka shima Salah ya zo da diyarshi filin wasan.Bayan kammala wasan an kuma bashi kyautarshi ta takalmin zinare, diyar ta Salah sai ta dauki kwallo ta ta fi da ita ta bugata a raga, wannan abu ya dauki hankulan mutane sosai ciki hadda mahaifin nata inda yayi ta dariya.
No comments:

Post a Comment