Tuesday, 7 May 2019

Dokar kirkiro sabbin masarautu ta tsallake karatun farko a Kano


Saki Muhammadu Sunusi na biyu
Kudurin dokar kirkirar sabbin masarautu ya tsallake karatu na farko a majalisar jihar kano.


Majalisar ta soma zaman nazari ne kan takardar da aka shigar gabanta na neman kirkirar sabbin masarautu hudu.
Majalisar dai na kokarin yiwa dokar masarautar ta 1984 ne kwaskwarima bayan bukatar da ta bayyana cewa wasu kungiyoyin sun shigar gabanta kan neman sake kirkirar masarautu a Jihar.
Sai dai tun kafin a fara zaman majalisar mutanen kananan hukumomin garuruwan da za a daga hakimansu, suka yiwa majalisar dafifi da zummar nuna goyon bayan su ga majalisar bisa yunkurin da take yi.
Wani dan karamar hukumar Gaya, Lawan Sofe ya shaidawa BBC cewa "mun zo majalisar dokoki ne dan nuna goyon bayan mu ga yadda ake yunkurin dawo mana da martabar masaruatar mu wadda a bisa tarihi sarkin Gaya shi ma sarki ne kamar sarkin Kano wanda kuma aslin wadanda suka kafa garin Gaya 'yan uwa ne ga kanin wanda ya kafa garin Kano".
" Idan ance akwai siyasa a ciki to ai itama masarautar siyasa ce ta kafa ta, a dan haka masu cewa wai 'yan siyasa ne ke kokarin amfani damu dan biyan bukatunsu, ya rage nasu''
Majalisar ta soma zaman na yau ne da misalin 11 karkashin jagorancin shugaban majalisar Honorable Alhassan Rurum.
Fitattun 'yan siyasa kamar Alhaji Bashir Othman Tofa na daga cikin wadanda suka halarci zaman majalisar, inda aka alakanta zuwan nasa da wani yunkuri na shiga tsakani masarautar Kano da kuma Majalisar dan ganin an sami daidaito.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment