Saturday, 11 May 2019

Gandujene abu mafi muni da ya taba samun Kano, Diyar sarki Sanusi

Biyo bayan raba masarautar Kano zuwa gida 5, diyar Sarkin Kanon, Shahida ta caccaki gwamnan Kanon inda ta bayyanashi a matsayin mafi munun abin da ya taba samun jihar ta Kano.Duk da yake cewa Shahida ta cire wannan rubutu da ta yi amma 'yar uwarta, Fulani Siddika ta riga ta yadashi.Tace idan kuna so kuga me rashin asali ke jawowa, ku duba kuga abin Ganduje yake yi a Kano. Mutunin da bashi da daraja yakan so ya lalata duk wani abu me daraja da ya ci karo dashi. Ina fatan mahaifiyata ba zata ce na cire wannan ba dan ina son in bayyanashi. Gandujene abu mafi muni daya taba samun Kano. Allah ya rabamu da masifar Ganduje.

'Yar uwarta, Fulani Siddika ta bayyana cewa bata da abinda zata ce dan 'yar uwartata ta fadi duk abinda take da niyyar fada.

A wani rubutun da shahida ta sake yi ta bayyana cewa da zarar sarki ya kasa katabus akan wani abu dan tsoron rasa mukaminshi to ya sauke kanshi.


No comments:

Post a Comment