Saturday, 18 May 2019

Golden Shoe: 'Yan kwallon Turai da suka fi yawan kwallaye a bana

A yayin da kakar wasan 2018/2019 ta zo karshe, daya daga cikin abubuwan dake daukar hankulan masoya kwallon kafa shine takalmin zinaren da ake baiwa dan kwallon da yafi yawan kwallaye a nahiyar turai.Ana la'akari da wahalar cin kwallo a kowace gasa wajan tantance wanda za'a baiwa kyautar, lura da cewa wata gasar ta fi wata wahalar cin kwallo. Gasar Premier League, Bundesliga, League 1, da Seria A data Laliga ana ajiye ta a matsayi na 2. Yayin da sauran gasar turai ake ajiye a matsayi na 1.5.

Ana tara yawan kwallayen dan wasa da 1.5 ko kuma nunka ta sau 2.

Messi ne yafi kowane dan wasa yawan kwallaye da 34 sai kuma Kylian Mbappe dake da yawan kwallaye 30.
Ga taurarin 'yan kwallon da suka fi yawan kwallaye a bana kamar haka:

LIONEL MESSI 30
KYLIAN MBAPPE 34
FABIO QUAGLIARELLA 25
MBAYE DIAGNE 30
ROBERT LEWANDOWSKI 22
DUVAN ZAPATA 22
PIERRE-EMERICK AUBAMEYANG 22
SADIO MANE 22
MOHAMED SALAH 22
DUSAN TADIC 28

No comments:

Post a Comment