Sunday, 12 May 2019

Guardiola ya yabi Liverpool, Klopp ya aikawa da Man City gargadi

Bayan lashe kofin Premier karo na biyu a jere,me horas da 'yan wasan Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa wannan shine kofi mafi wahala da ya taba lashewa a tarihin shi na horas da kungiyoyi.Kofuna 10 Guardiola ya lashe a tarihinshi. Sannan ya kara da cewa yana taya Liverpool murna tare da jinjina musu domin sune suka zaburar dasu har suka jajirce wajan cin wannan kofin.

Saidai Me horas da 'yan wasan Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana cewa, Manchester City su sani cewa a kakar wasa me zuwa zasu dawo da karfinsu dan lashe kofin na Premier, kamar yanda Sky Sport ta ruwaito.

Klopp ya kara da cewa, Gwagwar maya da Kungiya iri  Man City ba abune me sauko ba ko kadan.

No comments:

Post a Comment