Saturday, 11 May 2019

Gyaran kundin tsarin mulki ya ba Gnassingbe ikon mulkar Togo zuwa 2030


media
Majalisar dokokin Togo ta amince da yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, inda a yanzu aka bai wa shugaban kasar mai ci Faure Gnassingbe damar ci gaba da kasancewa bisa mulki har zuwa shekarar 2030.

Gyaran kundin tsarin mulkin na nufin Shugaba Gnassingbe, na da damar sake tsaya takara sau biyu a shekarun 2020 da 2025, na tsawon shekaru biyar-biyar, duk da cewa ya shugabanci kasar ta Togo a wa’adi 3, tun bayan karbar mulki daga Mahaifinsa shekaru 14 da suka gabata.
Ilahirin ‘yan majalisu 90 da suka halarci zaman ne suka kada kuri’ar goyon bayan yiwa tsarin mulkin na Togo gyara, matakin da ya zarta kashi hudu bisa 5 na yawan ‘yan majalisun da ake bukata kafin aiwatar da kudurin.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment