Saturday, 11 May 2019

Harkar da na yi da Timaya ta ruguzani sosai: Na gane kuskurena,bani bashi har abada>>Ummi Zeezee

Allah sarki, Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta fitar da wata sanarwa me taba zuciya akan yanda ta yi mu'amala da tauraron mawakin kudu,Timaya a baya wanda tace ta yi nadamar hakan.A wani sako data fitar ta shafita na Istagram, Ummi ta bayyana cewa tana fatan wani babban jafa'i ya aukawa duk wanda ya kara mata maganar Timaya kuma duk wanda ya kara mata maganar Timaya sai ta yi blocking dinshi domin ba ita ba Timaya har abada insha Allah. Ko harkar da na yi dashi a baya kuskurene na yi a matsayi na ta 'yar Adam ajiza wanda yanzu kuma na gane kuskurena domin ni na kula bani da wani aibu a idon Duniya da ake zagina akai illa harka da na yi dashi kawai wanda hakan ya ruguzani sosai.

No comments:

Post a Comment