Monday, 13 May 2019

Hazard yace ya gayawa Chelsea aniyarshi ta komawa Madrid jira kawai yake: Real Madrid ta shirya tsaf dan sayenshi


Real Madrid set to officially announce Eden Hazard transfer from Chelsea in £86 deal
Bayan kammala wasan Chelsea da Leicester City jiya, lahadi da ya kare da sakamakon 0-0, tauraron dan wasa Chelsea, Eden Hazard ya tabbatar da shirinshi na komawa kungiyar Real Madrid da wasa.

Hazard ya gayawa manema labarai cewa, na riga na yanke shawara ina jirane kamar yanda ku da masoyana kuke jira, ya kara da cewa tuni ya gayawa Chelsea aniyarshi yanzu dai kawai yana jirane.

Yace, Muna da wasan Europa, bayan wasan to zamu ga abinda zai faru.

Bayan wasan karshe na Europa da Chelsea zata buga da Arsenal a ranar 29 ga watan Mayu, kafar watsa labaran faransa, L'Equipe ta bayyana cewa Real Madrid a hukumance zata sanar da sayen Hazard din akan kudi, Fan miliyan 86.

No comments:

Post a Comment