Tuesday, 14 May 2019

Irin talaucin dake kasarnan na damuna: Wasu daga cikin mu basu da tausai>>Shugaba Buhari

A jawabin da yayi wajan shan ruwan da ya shiryawa manyan jami'an gwamnatinshi, shugaban kasa, Muhammadu Buhari yace irin talaucin da yake ganin mutane a ciki idan yana zagaya kasarnan abin na damunshi.Shugaban ya bayyana cewa zaka ga almajiri da yagaggun kaya da gwanon roba yana yawo, yace mafi yawancinsu, shuwagabannin kasarnan sun gaza, kamata yayi su rika taimakawa talakawan Najeriya ta wajan fito da wani tsari da zai bayar da ilimi.

Ya kara da cewa wasu daga cikinsu basu da tausai, haka zasu yi ta rayuwarsu ba tare da damuwa da halin da sauran mutane ke ciki ba.

No comments:

Post a Comment