Saturday, 25 May 2019

JAWABIN SANATA MARAFA BAYAN HUKUNCIN KOTUN KOLI

A'uzubillahi minasshaidani rajim, Bismillahir Rahmanin Rahim.

Ina cikakkiyar godiya ga Allah S.W.A mai komi Mai kowa wanda ya nuna mana wannan rana ta Juma'a. Wanda Allah ya cika alkawarinsa zuwa gare mu mutanen jihar Zamfara, kamar yadda na sha fada wanda har wasu su na ganin kamar ban yi maganar daidai ba, zan kara maimaitawa.


A ranara 25 ga watan daya ranar da mai shari'a Bello Shinkafi yayi mana danyen hukunci a cikin garin Gusau na gayawa duk wanda yake da kunne kuma yake son ya ji cewa idan dai Allahn da muke bauta gaskiya ne akwai shi ba babu shi ba, na yi imani da cewa wannan hukunci da aka yi a cikin garin Gusau ba zai tsaya ba.

Na kuma fada a ranar nan cewa idan dai Allah shi ne ya fada a cikin alkur'ani Mai girma cewa ya haramta wa kansa zalunci kuma ya haramta tsakankaninmu, na tabbata na yi imani wannan hukunci da aka yi a Gusau ba zai tsaya ba.

Kuma sannu a hankali duk wanda yake da hannu a cikin wannan danyen hukunci da aka yi Allah zai tona asirinsa. Kuma idan Allah ya yadda Allah zai yi wa mutanen jihar Zamfara maganinsa.

To cikakkiyar godiya ta ga Allah mai komai mai kowa. Wanda shi ne yake bada mulki ga wanda yaso kuma ya amsa ga wanda ya so yau ya tabbatar da gaskiya kuma ya tabbatar da cewa abinda muke fada shi ne gaskiya.

Na biyu, ina godiya ga shugaban kasa Muhammad Buhari, bisa dattakon da ya yi na kin kama karya. Babu abinda wadannan mutane ba su yi ba, domin su jawo shi a cikin wannan magana domin su sa ya tsoma baki domin a yi mana karan tsaye a karya mu kota kowanne hali, Allah da ikonsa ya sa maigirma shugaban kasa tunda aka fara wannan magana bai taba tsoma bakin shi ba domin ya ce a taimaki wane ko kuma kada a taimaki wane, duk da.
Daga Zubairu Haruna Tela Madogara
Rariya.


No comments:

Post a Comment