Pages

Sunday 19 May 2019

Jima'i ya ragu a tsakanin matasa>>Bincike

''Ana jima'i a duniya.'' kamar yadda jama'a ke yawan ambata.

Amma kamar yadda wani sabon rahoto da wasu cibiyoyin bincike na kasashen Birtaniya da Amurka suka bayyana, suna ganin cewa matasa maza na wannan zamanin sun fi mayar da hankali kan wasannin Game na talabijin da kuma kallon fina-finai a shafukan intanet fiye da yin jima'i.


Raguwar jima'i a Amurka
A wani bincike da wata cibiyar bincike ta jami'ar Chicago da ke Amurka ta gudanar, ta bayyana cewa matasa maza na shekarun baya sun fi jima'i fiye da na yanzu.

A binciken mai suna ''General Social Survey,''- an gudanar da hirarraki da dubban mutane kuma an fara gudanar da irin wannan binciken tun shekarar 1972 inda kuma ake ci gaba da yi a kai a kai.

Binciken na kwananan ya bayyana cewa kashi 23 cikin 100 na balagaggun da aka tattauna da su ba su yi jima'i ba a watanni 12 da suka wuce- kason ya ninka sau biyu cikin shekaru 10- kuma akasarinsu maza ne.

Kamar yadda bincken ya nuna, kason maza da ke kasa da shekaru 30 wadanda suka ce ba su yi jima'i ba a shekarar da ta gabata ya ninka sau uku tun 2008 zuwa kashi 28 cikin 100- wanda hakan ya nuna yawan ya karu sosai a maza fiye da mata da suke shekaru daya da mazan.

Binciken ya kuma ce fiye da rabin balagaggun da ke Amurka da suke tsakanin shekara 18 zuwa 34 ba su da abokan zama- wannan yawan ya karu da kusan kashi 33 a 2004.

'Yan Birtaniya ma sun rage jima'i


Irin wannan lamarin na raguwar jima'i musamman a matasa maza da mata na faruwa a Birtaniya.

A wani bincike da wata mujallar Birtaniya mai wallafa labarai kan lafiya ta gudanar, ta tattara bayanai kan wannan lamari.

Binciken an fara shi ne tun 1990 wanda aka rinka yinsa duk bayan shekara 10 ya tattauna da kusan mutane dubu 45, inda suka ba da bayani kan rayuwar jima'insu a Birtaniya.

Kamar yadda mujallar ta bayyana, maza da mata da dama ba su yi jima'i ba a watannin da suka gabata; inda rabin maza da mata 'yan shekara 16 zuwa 44 suna jima'i akalla sau daya a mako.

Wannan abin ya ci gaba da karuwa sama da shekaru 25 ke nan, kuma ma'aurata da suka yi aure suna zama tare sun bayyana cewa yawan jima'in da suke yi shekaru 20 da suka wuce ya ragu.

Me ke sa tsofaffin mutane na rage jima'i?

Masu bincike sun bayyana cewa raguwar jima'i a Birtaniya ya ragu ne musamman a mutanen da suke jima'i sosai a da, maimakon wadanda ba su taba yin jima'in ba.

Farfesa Simon daga cibiyar kiwon lafiya ta jami'ar Newcastle ya bayyana cewa sauye-sauye da aka samu musamman na gudanar da rayuwa a shekarun da suka shude sun taka rawa wajen kawo cikas ga raguwar jima'i.

Ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da ya sa ake samun raguwar jima'i ga matasa akwai rashin auren wuri, inda matasan ba su tashi fara jima'in, sai sun kai shekaru 30.

Ya kuma bayyana cewa yawan kallon fina-finan batsa na tasiri ga rayuwar ma'aurata kan yin jima'i.

Farfesan ya ce idan mutum na bata lokacinsa wajen kallon fina-finan jima'i, mutum ba zai samu lokac ba wajen yin jima'i a aikace.

A wani bincike da BBC ta gudanar a Birtaniya inda aka yi tambayoyi ga fiye da mutum 1000 'yan shekara 18 zuwa 25 inda binciken ya bayyana cewa, kashi 55 cikin 100 suka tabbatar da cewa ta hanyar kallon fina-finan batsa suka samu wayewa kan jima'i.

Wani abu zai iya dauke maku hankali daga yin jima'i?

''Akwai abubuwan yi da dama da ake yi a halin yanzu da misalin karfe 10:00 na dare ba kamar shekaru 20 da suka gabata ba, in ji Jean Twenge, wata farfesa kan dabi'un bil adama da ke jami'ar San Diego ta bayyana.''

Farfesa Twenge na ganin wasannin Game din talabijin da kuma shafukan kallon fina-finai na intanet na bayar da gudummawar haka.

A wata hira da ta yi da jaridar ''Washington Post,'' ta bayyana cewa lokacin da ake shafewa wurin yin jima'i na goggayya da lokacin da ake shafewa wajen kallo da shafukan sada zumunta.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment