Friday, 10 May 2019

Juventus za ta raba gari da kocinta

Kocin Juventus Massimiliano Allgeri ya yanke shawarar rabuwa da kungiyar bayan karkare kakar wasa ta bana, bayan shafe shekaru 5 yana horar da zakarun na gasar Seria a Italiya.Jaridar La Stampa ta kasar Italiya da ake wallafa ta a birnin Turin ce ta rawaito cimma yarjejeniyar rabuwar da Allegri yayi da Juventus, ko da yake ba ta yi karin bayani akan abinda yarjejeniyar ta kunsa ba.

A baya dai kungiyoyin Chelsea da Arsenal sun yi kokarin daukar hayar kocin na Juventus mai shekaru 51, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

A halin yanzu kuma kungiyar Paris saint germain ke neman daukar Massimiliano Allegri, don maye gurbin kocinta Thomas Tuchel da take shirin kora.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment