Tuesday, 14 May 2019

Ka caje dan sanda kamin ya caje ka>>Hukumar 'yansanda

Hukumar 'yansandan Najeriya ta bayyana cewa 'yan Najeriya nada damar su caje dan sanda kamin ya cajesu.A wata sanarwa da me magana da yawun 'yansandan Frank Mba ya fitar ya bayyana cewa idan dan sanda yazo zai yi bincike a gidanka ko kuma motarka ko kai kanka, to kana da damar cajeshi tukuna dan kada a saka maka abinda baka dashi, saidai ya shawarci a bukaci hakan cikin kalamai masu dadi.

Ya kuma ce mutum na da damar ya tambayi dalilin da yasa za'a kamashi, kamin a kamashi, hakanan kana damar bukatar a barka ka kira wani na kusa da kai ko kuma lauyanka ka sanar dashi bayan an kamaka dan kada ayi tsammanin bacewa ka yi.

Hukumar 'yansandan ta kuma bayar da shawarar cewa kada mutum yayi gigin kin yadda a kamashi koda kuwa yana tunanin cewa kamun nashi ba bisa adalci bane. Sannan kada yayi katsalandan idan yaga ana kokarin kama wani.

No comments:

Post a Comment