Monday, 13 May 2019

Ka sauka daga mukaminka ko in saukeka>>Gwamna Ganduje ya gayawa sarki Sanusi


Wasu rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa, gwamna Ganduje ya baiwa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi zabi guda 3 akan dambarwar raba masarautar dake faruwa inda ya bukaci ya zabi guda daga ciki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, bayan da sarki Sanusi ya lura da cewa gwamnan nada shirin kirkiro karin masarautu a jihar da kuma bincikar masarautar akan wasu kudade da aka kashe ba tare da amincewar gwamnatin jihar ba sai ya tura Dangote ya roki gwamnan dan ya janye wannan aniya tashi. Rahoton yace Gwamna Ganduje a wancan lokacin ya gayawa Dangote cewa yaje ya gayawa Sarki Sanusi cewa yana da zabi uku, kodai ya sauka daga mukaminshi ko kuma Gwamnan ya saukeshi ko kuma a kirkiro karin masarautu a jihar tunda sarkin ya zabi ya nunawa wani bangaren siyasa goyon baya.

Rahoton yace in banda shiga tsakanin na Dangote da tuni Gwamna Ganduje ya sauke sarki Sanusi daga mukaminshi.

Hakanan rahoton yace har yanzu tana kasa tana dabo dan kuwa akwai shirin mayar da sarki Sanusi daya daga cikin sabbin masarautun da aka kirkiro sannan a dawo da daya daga cikin sarakunan masarautar Kanon.

Hakanan wata majiya daga hukumar hana rashawa ta Kano dake bincikar masarautar Kanon akan kashe kudi ba tare da amincewar gwamnatin jiha ba tace, binciken yana harin sarki Sanusi ne dan kuwa zata kai matsayin da za'a mayar da lamarin kotu inda za'a bukaci sarkin da ya zo ya kare kanshi.

No comments:

Post a Comment