Tuesday, 7 May 2019

Kalaman Buhari kan tsaro sun jawo ce-ce-ku-ce

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban sufeton 'yan sanda kasar na kokari matuka wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar kasar.


Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya dawo kasar bayan kwashe kwanaki 10 a birnin Landan.

Shugaban ya ce "ga duk wanda ya san sufeton 'yan sanda to zai fuskanci ya rame sosai saboda tsabar aikin da yake yi."

Hakazalika a lokacin da dan jaridar tashar talabijin din kasar NTA ya yi masa tambaya kan kafa sabuwar gwamnati, Buhari ya amsa da cewa "ba zan ce komai a kai ba."


Sai dai wadannan kalaman nan shugaban sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta a kasar.

Wasu suna ganin bai kamata shugaban ya yi su ba, ganin yadda ake ci gaba da kashe-kashe a kasar da kuma yadda ake satar mutane don neman kudin fansa ba dare, ba rana a jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.

Cikin kwanaki da shugaban ya shafe baya kasar an samu matsaloli tsaro da dama da garkuwa da mutane baya ga hare-hare da suka yi sanadi mutuwar mutane.

"Wannan abin kunya ne, dubi wanda yake shugabancin kasar da ake kira giwar nahiyar Afirka," in ji Real Nwa Mazi.

"Buhari ya yarda cewa ramar babban sufeton 'yan sanda tana nuna yadda ya dukufa ga aikinsa? Wace irin rashin basira ce haka!"

"Dalilai da dama za su iya jawo rama ciki har da rashin lafiya da yunwa wadda ta yi yawa a kasar. Ya kamata Buhari ya dauki batun tsaro da muhimmanci," in ji wata Victoria P. Abraham.

Abubuwan da suka faru bayan tafiyar Buhari Landan:
'Yan bindiga sun kai hari mahaifar Shugaba Buhari
'Yan bindiga sun kai hari 'makarantar mata' a Zamfara
'Yan fashi sun kashe sama da mutum 30 a Zamfara
An yi jana'izar mutum 14 a Katsina
Shugaban UBEC ya kubuta daga hannun masu garkuwa
'Yan sanda sun mutu yayin sace ma'aikatan mai.
Ita ma tafiyar Buhari Landan ta ja ce-ce-ku-ce musamman tsakanin al'ummar kasar da suke nemi jin dalila tafiyarsa can.

Sai dai kamar yadda mai magana da yawun Shugaban, Malam Garba Shehu ya bayyana ''shugaban ya rinka gudanar da aiki daga Landan, domin kuwa ba hutu ya tafi yi ba''.

Mutane da dama na ganin cewa shugaban ya je ganin likitoci ne kamar yadda ya saba, amma fadarsa ta musanta hakan.

A shekarar 2017, Shugaba Buhari ya yi jinya tsawon kusan wata uku a Birtaniya, inda ba a san takamaimai ciwon da ya yi ba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment